IQNA

Dakarun Iraki Sun Kara Samun Nasarar Halaka Wasu ‘Yan Ta’addan Daesh 22

23:55 - January 29, 2021
Lambar Labari: 3485600
Tehran (IQNA) dakarun kasar Iraki sun kara samun nasarar halaka wasu ‘yan ta’addan takfiriyya na kungiyar Daesh su 22 a yau.

Tashar Akbarul Iraq ta bayar rahoton cewa, dakarun hadin gwaiwa na kasar Iraki, da suka hada da sojoji da kuma dakarun sa kai na Hasd Al-shaabi, sun kara samun nasarar halaka wasu ‘yan ta’addan takfiriyya na kungiyar Daesh su 22 a yau a cikin lardin Karkuk.

Rahoton ya ce, wannan na zuwa ne a karkashin farmakin da sojoji da kuma dakarun sa kai na Hasd Al-shaabi suka fara kaddamarwa ne a kan ‘yan ta’addan Daesh da suke neman sake farfadowa a cikin kasar Iraki, tare da taimakon Amurka da kuma wasu gwamnatocin larabawa masu masu mara baya ga kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Faramakin dai yana gudana a cikin nasara, inda bayan halaka wannan adadi na ‘yan ta’adda, an kuma samu wasu daga cikin kayayyakin da suke amfani da su wajen kai hare-haren ta’addanci, da suka hada da bindigogi da kuma nakiyoyi gami da motoci.

Koa jiya ma Frayi ministan kasar ta Iraki Mustafa Alkazimi ya sanar da cewa, an halaka matamakin shugaban kungiyar da Daesh a cikin kasar Iraki a karkashin wannan farmaki da aka fara kaddamarwa.

 

3950552

 

 

 

captcha