IQNA

Dakarun Hizbullah Sun Kakkabo Jirgin Leken Asirin Isra’ila A Kudancin Kasar Lebanon

23:34 - February 02, 2021
Lambar Labari: 3485614
Tehran (IQNA) mayakan kungiyar Hezbollah sun sanar da kakkabo wani jirgin leken asirin Isra’ila da ya shiga cikin Lebanon daga kudancin kasar.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar ta fitar, ta sanar da cewa wani jirgin leken asirin Isra’ila ya shigo cikin kasar Lebanaon daga iyakokin kudancin kasar, kuma mayakan kungiyar suka kakkabo shi ba tare da bata lokaci ba.

Haka nan kuma wasu daga cikin kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton  bacewar jirgin leken asirin Isra’ila  a cikin kasar Lebanon, kamar yadda kakakin rundunar sojin yahudawan Isra’ila ma ya tabbatar da hakan, inda ya ce jirgin ya fadi a kudancin kasar Lebanon ba tare da wani Karin bayani ba.

A halin yanzu dai kungiyar Hizbullah bisa bayanin da ta fitar, tana da kyakkyawan shiri na tunkarar irin wadannan ayyuka na tsokana da Isra’ila take yi a kan kasar Lebanon.

Kungiyar ta tabbatar da cewa za ta iya mayar da mummunan martani a cikin Isra’ila da makamai masu linzami, matukar dai ta yi gigin sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Lebanon.

3951404

 

 

 

 

captcha