IQNA

Dakin Ajiye Kayan Tarihi na Birnin Madina Na Bayyana Wani Bangare Kan Rayuwar Ma'aiki (SAW)

22:46 - February 07, 2021
Lambar Labari: 3485627
Tehran (IQNA) dakin ajiye kayan tarihi na birnin Madina yana a matsayin wurin da ke bayyana wasu bangarori an rayuwar ma'aiki (SAW)

Shafin yada labartai na Arab News ya bayar da rahoton cewa, an bude baje kolin kasa da kasa a babban dakin ajiye kayan tarihi na birnin Madina da ke bayyana wasu daga abubuwa da suka shafi tarihin muslunci da kuma rayuwar ma'aiki (SAW)

An bude wanann babban baje koli na kayayyakin tarihin musuluncia  wanann wuri ne tare da halartar wasu daga cikin jami'ai na gwamnatin Saudiyya, da suka hada da yarima Faisal Bin Salman.

Cibiyar sanya ido kan kayayyakin tarihin musulunci ta MWL da ke karkashin kungiyar kasashen musulmi ce take kula da wannan wuri.

Wannnan babban wuri yana gefen masallacin manzon Allah (SAW) ne da ke birnin na Madina, wanda yake bude tsawon sa'oi 24 na kowace rana.

Yarima Faisal ya bayyana cewa, wannan wuri yana a matsayin wurin da yake bayyana wasu daga cikin ababe na tarihi da ke komawa zuwa lokacin ma'aiki (SAW) a birnin na Madina.

موزه بین‌المللی مدینه؛ آیینه سیره نبوی + فیلم

موزه بین‌المللی مدینه؛ آیینه سیره نبوی + فیلم

موزه بین‌المللی مدینه؛ آیینه سیره نبوی + فیلم

3952422

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: birnin madina kayan tarihin muslunci
captcha