IQNA

Rageb Mustafa Galwash Ya Fara Karatun Kur'ani A Gidan Radiyon Masar Tun A Kuruciyarsa

22:57 - February 07, 2021
Lambar Labari: 3485629
Tehran (IQNA) fitaccen makarancin kur'ani Rageb Mustafa Galwash ya fara karatun kur'ani mai tsarki a gidan radiyon masar tun yana matashi.

Mustafa Galwash an haife shi ne a kauyen Barma da ke cikin gundumar Tanta a Kasar Masar a ranar 5 ga watan Yunin shekara ta 1938.

Daga cikin malamansa akwai Abdulganiy Al-sharqawi, sai kuma Ibrahim Al-tabhili gami da Ibrahim, sai kuma a cikin makaranta na Masar da kuma kasashen shi ma akwai masu koyi da salon karatunsa.

Yana da yara guda hudu da suka hada da maza biyu da kuma mata biyu, wadanda dukkaninsu ya ba su tarbiya ta kur'ani mai tsarki.

Masallacin Ahmadi shi ne masallacin da yafi shahara wajen karatunsa, wanda kuma a nan ya koyi wasu ilmomin kur'ani tun yana matashi a hannun sheikh  Ibrahim Al-tabhili daya daga cikin malamansa.

3952279

 

captcha