IQNA

Ansarullah: Makiya Sun Mayar Da Maarib Wani Babban Sansani Na Daesh Da Alqaeeda

23:55 - March 03, 2021
Lambar Labari: 3485710
Tehran (IQNA) kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ta bayyana cewa makiya sun mayar da yankin Maarib a matsayin wata matattara da ‘yan ta’adda.

Tashar Almasirah ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin Amurka tana ci gaba da bayar da dukkanin taimako ga abokan kawancenta masu yaki a kan al’ummar kasar Yemen.

Bayanin ya ce Saudiyya tare da taimakon Amurka, sun mayar da yankin Maarib wani babban sansani na mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda na Alqaeeda da kuma Daesh, wadanda su ne suke yi musu yaki a yankin a halin yanzu.

Tun kafin wannan lokacin dai kungiyar alqaeeda tana sansanoni a cikin kasar Yemen, wanda hakan ne dalilin shigar Amurka  akasar tun shekarun baya da sunan yaki da alqaeeda, inda  a halin yanzu kuma suke amfani da alqaeeda da Daesh wajen yaki a kan al'ummar Yemen da taki mika musu wuya.

Dangane dafurucin da sabbin mahukuntan Amurka ke yi kan dakatar da yaki a kan kasar Yemen, bayanin na Ansarullah ya ce wannan siyasa ce, domin nuna duniya cewa su masu son sulhu ne da zaman lafiya, amma lokaci guda suna taimaka Saudiyya wajen yin kisan kiyashi a kan fararen hula a kasar Yemen.

Bayanin ya ce da sabbin mahukuntan gwamnatin Amurka sun ga dama, a rana daya za su ba Saudiyya umarni kan ta dakatar da yaki a kan Yemen, kuma a ranar za ta dakatar tana rawar jiki, domin kuwa ba za ta iya saba wa umarininsu ba.

3957498

 

 

captcha