IQNA

An Yi Ganawa Ta Tarihi Tsakanin Paparoma Francis Da Ayatollah Sistani A Iraki

21:48 - March 06, 2021
Lambar Labari: 3485720
Tehran (IQNA) an yi ganawa ta tarihi a yau tsakanin Paparoma Francis da kuma Babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sistani a birnin najaf.
A ziyarar aiki ta kwanaki uku kuma na farko da shugaban mabiya addinin kirista na darikar  Katolika yake kaiwa a kasar Iraki a karon farko a tarihi, ya gana a yau Asabar tare da bababn malamin addinin muslunci an kasar Ayatollah Sayyid Ali Sistani.
 
Shuwagabannin biyu sun gana na tsawon kimanin sa’a guda, kuma sun tattuna kan fahimtar juna da rayuwa tare tsakanin mabiya addidai daban-daban a kasar Iraki da yankin gabas ta tsakiya da kuma sauran kasashen duniya.
 
Jami’an tsaro na kasar ta Iraki, na sama da na kasa kimanin dubu goma ne aka jibge domin tabbatar da tsaro a wannan ziyarar tarihi wadda Paparoma ya ke gudanarwa a kasar ta Iraki.
 
A yau dai bayan Paparoma ya gana da Ayatollah Sistani, ya kuma kai ziyara a garin Ur na annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi, inda ya gana da mabiya addinai daban-daban.
 
Sai kuma gobe Lahadi ana sa ran Paparoma zai tafi birnin Arbil na yankin Kurdistan na kasar ta Iraki, sannan zai kammala ziyarar a ranar Litinin bayan ziyarar wasu majami'ioi na tarihi a birnin Musil, wadanda ‘yan ta’adda suka mamaye su a lokutan baya.
 
Dangane da wannan ziyara, ofishin Ayatollah Ali Sistani ya bayyana a shafinsa na yanar gizo kan cewa, kiristoci a kasar Iraki za su ci gaba da rayuwa da sauran mutanen kasar kamar yadda sauran ‘yan kasar suke rayuwa.

 

captcha