IQNA

Tawagar Mabiya Addinin Kirista Ta Halarci Taron Bude Wani Sabon Masallaci A Masar

23:46 - March 07, 2021
Lambar Labari: 3485722
Tehran (IQNA) wata tagawar mabiya addinin kirista a kasar Masar ta halarci taron bude wani masallaci a kasar Masar.

shafin Misrul Yaum ya bayar da rahoton cewa, a yau wata tagawar mabiya addinin kirista a yankin Sinai a kasar Masar ta halarci taron bude wani masallaci tare da bayar da kyautar kwafin kur'ani.

Wannan tawagar ta kunshi manyan malaman addinin kirista daga yankin, inda suka halarci taron bude sabon masallacin da nufin kara karfafa alaka ta zaman lafiya tsakaninsu da mabiya addinin musulunci.

Muta'il Qoms Zakhari shugaban majami'ar kiristoci ta Dulaji, ya bayar da kyautar kwafin kur'ani mai tsarki ga daraktan hukumar kula da harkokin musulunci reshen yankin Sinai Hassan Amir.

Wannan yana faruwa a daidai lokacin shugaban mabiya addinin kirista na darikar katolika yake gudanar da wata ziyara a kasar Iraki inda yake ganawa da malaman addinin musulunci da kuma na addinin kirista da sauran bangarori na al'ummar kasar.

3958053

 

captcha