IQNA

MDD, Ta Bukaci Janyewar Dakarun Kasashen Waje A Libiya Ba

19:19 - March 13, 2021
Lambar Labari: 3485740
Tehran (IQNA) Kwamitin Tsaron na MDD, ya bukaci janyewar dakarun kasa da kasa da mayaka dake Libiya ba tare da wata ba.

A kudirin da galibin mambobin kwamitin suka amince da shi a jiya Juma’a, ya bukaci janyewar duk dakarun dake Libiya.

Kwamitin ya kuma yi maraba da yadda majalisar Libiyar ta amince da sabuwar gwmnatin hadin kai da aka kafa.

Haka kuka kwamitin ya bukaci dukkan bangarorin dake riki a kasar dasu aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a ranar 23 ga watan Oktoban bara.

A hannu guda kuma kwamitin ya bukaci da a mutunta yarjejeniyar hana shigar da makamai a kasar ta Libiya.

Alkalumman da MDD, ta fitar sun nuna cewa kimanin dakaru da mayaka 20,000 ke jibge a kasar ta Libiya, a kasrehn shekarar 2020 data gabata, kuma har yanzu ba’a samu rahoton janyewar dakarun ba.

http://hausatv.com

captcha