IQNA

An Fara Raba Ruwan Zamzam Ga Masu Ziyara A Masallacin Haramin Makka Mai Alfarma

15:08 - March 24, 2021
Lambar Labari: 3485761
Tehran (IQNA) mahukuntan kasar Saudiyya sun fara raba ruwan zamzam ga masu ziyara a masallacin haramin Makka.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a jiya ne mahukuntan kasar Saudiyya sun fara raba ruwan zamzam ga masu ziyara a masallacin haramin Makka mai alfarma musamman ganin cewa lokacin azumin watan Ramadan an karatowa.

Abdulrahman Bin Abdulaziz Al-sudais shi ne shugaban cibiyar da ke kula da haramomin Makka da Madina, ya bayyana cewa an fara bayar da ruwan zamzam ga masu ziyara a masallacin harami ne, saboda karatowar lokacin ibadar watan Ramadan mai alfarma.

Ya ce an ci gaba da wannan aiki daga jiya, bayan dakatar da shi fiye da shekara guda da ta gabata, sakamakon bullar cutar corona, kuma ana raba ruwan zamzam ne ta hanyoyin da suka dace, tare da kiyaye kaidoji na kiwon lafiya da tsafta.

Ya kara da cewa za a ci gaba da gudanar da wannn sharia  kowace rana, tun daga bayan sallar zuhur har zuwa karfe 9 na dare a kowace rana.

An dauki kwararan matakai na kariya daga cutar corona, saboda gudanar da ayyukan iibada a cikin watan Ramadan mai alfarma a masallacin haramin Makka mai alfarma, da kuma masallacin manzon Allah tsita da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa da ke Madina.

3960941

 

 

 

 

captcha