IQNA

Ana Gab Da Kammala Gyaran Kyallen Dakin Ka’aba Mai Alfarma A Shirye-Shiryen Watan Ramadan

21:34 - April 10, 2021
Lambar Labari: 3485794
Tehran (IQNA) an mkusa kamala gyaran kyallen dakin Ka’aba mai alfarma a shirye-shiryen shiga watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya nakalto daga jami’an gwamnatin kasar Saudiyya cewa, ana ci gaba da gyaran kyallen dakin Ka’aba mai alfarma a shirye-shiryen shiga watan Ramadan na wannan shekara, wanda kuma ana gab da kamala aikin.

Wannan dai yana daga cikin ayyukan da ake yi a kowace shekara, a daidai lokacin da ake shirin shiga watan azumi, ana gyara kyallen dakin Ka’aba, tare da dinke wuraren da ya kece ko kuma wanke wuaren da ya yi datti.

Ana gudanar da aikin ne tare da wasu kwarru 14 da suka kware wajen gudanar da irin wannan aiki, sai kuma sauran masu taimaka musu.

A daya bangaren kuma hukumar da ke kula da harkokin da suka shafi haramin Makka da Madina ta sanar da cewa, a wannan shekara akwai sabbin shirye da za a gudanar a dukkanin haramomin biyu masu alfarma.

A masallacin haramin Makka akwai shirii na ilmantarwa, wanda zai shafi lamurran kur’ani da kuma amsa tambayoyi da suka shafi addini, wanda zai zama kai tsaye ne amma ta hanyoyin yanar gizo.

Baya ga haka kuma akwai baje koli kan lamurran da suka shafi kur’ani, wanda za a gudanar a wani wuri da aka kebancea  cikin masallacin haramin Makka.

Haka nan kuma a masallacin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ke Madina, akwai wasu shirye-shiryen makamantan wannan, duk a  cikin watan Ramadan mai alfarma.

3962666

 

captcha