IQNA

Furucin Wani Malami A Masar Ya Bar Baya Da Kura Inda Ya Ce Akwai Sarakunan Fir’aunoni Musulmi

23:44 - April 11, 2021
Lambar Labari: 3485798
Tehran (IQNA) Furucin da wani daya daga cikin fitattun malamai na kasar Masar ya yi kan cewa akwai sarakunan fir’anoni muminai ya bar bayar da kura.

Rahotanni daga kasar Masar na cewa, kalaman da wani daya daga cikin fitattun malamai na kasar ya yi da ke cewa akwai sarakunan fir’anoni muminai ya bar bayar da kura tare da jawo ce-ce-ku-ce a kasar baki daya.

Khalid Aljundi daya ne daga cikin mambobin kwamitin manyan malamai da ke kula da lamurran da suka shafi addinin mulsunci a kasar Masar, shi ne ya bayyana hakan a cikin wani shirin tattaunawa na talabijin mai suna DMC.

A cikin bayanin nasa ya furta cewa, a cikin sarakunan Fir’anoni da aka yi a kasar Masar a  tarihi akwai muminai wadanda suka mika lamarinsu ga Allah, kuma suna bin umarnin allah da nisantar haninsa.

Malamin ya buga misali da wani mumini daga cikin mutanen Fir’auna wanda aka kawo labarinsa a cikin kur’ani, ya ce wannan na daga cikin misalai da suke nuni da cewa akwai muminai daga cikin fir’anoni kuma suna alfahari da iyayensu fir’anoni muminai.

Sai wannan furuci na wannan babban malami na kasar Masar yana ci gaba da fuskantar kakkausan martani daga jama’a a kasar ta Masar, tare da bayyana abin da ya ambata da cewa babban kure ne, domin kuwa babu inda aka ambaci haka a cikin kur’ani ko kuma tabbataccen tarihi.

Haka nan kuma dangane da ayar mumini daga jama’ar Fir’auna wato aya ta 18 a cikin surat Ghafir, tana Magana ne akan wani mutum mumini daga mutanen Fir’auna wanda ya boye imaninsa, kuma ya bayyana imaninsa a lokacin da ya ga za a cutar da annabi Musa (AS) amma shi akan kansa ba Fir’auna ba ne kamar yadda malamin yake neman tabbatarwa.

3963390

 

 

 

 

 

 

 

captcha