IQNA

Jagoran Juyi Na Iran: Matsayin Kasarmu Kan Yarjejeniyar Nukiliya A Bayyane Yake

23:39 - April 15, 2021
Lambar Labari: 3485810
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Muslunci na Iran ya bukaci da kada a ja dogon lokaci a tattaunawar da ake yi da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliya.

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya bukaci da kada a ja dogon lokaci a tattaunawar dake gudana da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.

Ayatollah Khamenei, ya kuma jaddada cewa, Iran ba zata dakatar da matakan da take dauka ba game da yarjejeniyar har sai ta gani a zahiri, cewa Amurka, ta dage ma ta gabadayen takunkuman data kakaba.

Jagoran ya fada a jiya Laraba cewa, ya baiwa jami’an diflomatsiyan Iran umarnin su ci gaba da tattaunawa, amma tare sanin cewa ba za’a dawwama har kulun ba kan tattaunawa.

Ya cce; ‘’ba za’a dawwama kan tattaunawa ba har illah masha Allahu, a cewar jagoran, don kada hakan ya zama wata hanya da sauren bangarorin da ke cikin yarjejeniyar zasu amfana da ita domin tsawaita yarjejeniyar ko da yaushe.

Kalaman na jagoran juyin juya halin musulincin na Iran, na zuwa ne a daidai lokacin da tawagar Iran, da karamin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ke jagoranta ta isa a birnin Vienna na kasar Austrea, domin ci gaba da tattaunawa da sauren bangarorin dake cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015.

Kasashen dai sun hada da Buritaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, a wani mataki na lalubo hanyar da Amurka zata koma cikin yarjejeniyar da tsohon shugaba Donald Trump, ya janye Amurka data ciki a 2018, da kuma yadda za’a dagewa Iran jerin takunkuman da aka kakaba mata.

 

3964657

 

 

 

 

 

 

captcha