IQNA

Mutane Dubu Hudu Sun Wanke Dakin Ka’abah Da Farfajiyar Masallacin Harami Mai Tsarki A Cikin Mintuna Biyar

23:42 - April 15, 2021
Lambar Labari: 3485811
Tehran (IQNA) a karon farko a tarihi an gudanar da aikin wanked akin Ka’aba da farfajiyar masallacin harami mai tsarki a cikin lokaci mafi karanci.

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, a karon farko a tarihi an gudanar da aikin wanked akin Ka’aba da farfajiyar masallacin harami mai tsarki a cikin lokaci mafi karanci, inda ma’aikatan da suke kula da tsaftar wurare masu tsarki su kimanin dubu hudu suka gudanar da aikin a cikin kasa da mintuna biyar suka kamala.

A cewar mahukuntan ad suke da haramomi masu tsarki na Makka da Madina, wannan shi ne karon farko da aka taba yin irin wannan aiki a cikin kankanin lokaci a tarihi.

Kimanin mutane 291 ne suke tattara sharar da aka tara tare da zubar da ita ba tare da bata lokaci ba.

Haka nan kuma an yi amfani da manyan motoci da kuma bokitai na tattara shara guda 1500 a lokacin aikin.

https://iqna.ir/fa/news/3964770

 

 

 

captcha