IQNA

Hamas Ta Kirayi Gwamnatin Saudiyya Da Ta Saki Falastinawa Da Ta Kame Ta Tsare Su A Kurkuku Ba Tare Da Wani Laifi Ba

23:45 - April 15, 2021
Lambar Labari: 3485812
Tehran (IQNA) Kungiyar gwagwarmayar falastinawa ta kirayi gwamnatin Saudiyya da ta saki Falastinawa da ta kame ta tsare su a kurkuku ba tare da sun aikata wani laifi ba.

Kakakin kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa, Hamas, Hazim Kassim, ya bayyana cewa; Babu wani dalili da zai sa Saudiyyar ta ci gaba da tsare Muhammad al-Khidry da dansa da kuma ‘yan’uwansa Palasdinawa a cikin kurkukun kasar.”

Hazim Kassim ya kuma ce; Babu wani dalili da zai sa a ci gaba da tsare Palasdinawan ba tare da an tuhume su da wani laifi ba, hakan wani laifi ne babba.

Kungiyar ta Hamas dai ta sha yin kira ga Saudiyyar da ta saki al-kidhry wanda yake fama da cutuka masu hatsari tare da sauran wadanda take tsare da su.

Mahukuntan na Saudiyyar sun kame Muhammadu al-Kidhry ne tun a watan Disamba na 2019 tare da dansa da wasu tarin Palasdinawa ba tare da wani dalili ba da ya wuce kasantuwar mambobi a kungiyar ta Hamas.

 

 

 

3964807

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha