IQNA

UAE Ta Aike Wa Isra'la Da Sakon Taya Murna Na Zagayowar Lokacin Da Yahudawa Suka Mamaye Falastinu

23:45 - April 16, 2021
Lambar Labari: 3485814
Tehran (IQNA) gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ta aike wa gwamnatin yahudawan Isra'ila da sakon taya murna kan cikar shekaru 73 da yahudawa suka mamaye Falastinu suka kafa Isra'ila.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ta aike wa gwamnatin yahudawan Isra'ila da sakon taya murna kan cikar shekaru 73 da yahudawa suka mamaye Falastinu suka kafa Isra'ila a cikin yankunan Falastinawa.

Wannan lamari yana ci gaba da shan kakkausar suka da martani daga larabawa da musulmi a shafukan yanar gizo, inda da dama suke bayyana hakan a matsayin cin amana mafi muni ga al'ummar falastinu da musulmi da hadaddiyar daular larabawa UAE ta yi.

Gwamnatin yahudawan Isra'ila ta mayar da wannan rana da ta mamaye Falastinu tare da kafa Isra'ila a matsayin ranar idin kasa, lamarin da ya farua  cikin shekara ta 1948.

A lokacin dai yahudawa da suka zo daga kasashen duniya daban-daban tare da taimakon Ingila, sun kori Falastinawa daga garuruwa 20 da kuma kauyuka 400, inda suka mamaye su, suka mayar da su nasu, baya ga haka kuma suka kashe wasu dubban Falastinawa tare da mayar da wasu miliyoyi 'yan gudun hijira kafin su kafa Isra'ila.

 

3964913

 

 

captcha