IQNA

Ayyukan Watan Ramadan Tsari Ne A Cikin Dukkanin Rayuwar Dan adam

23:43 - April 18, 2021
Lambar Labari: 3485821
Tehran (IQNA) ayyukan ibada da suke cikin watan ramadan tsari ne ga dukkanin sauran kwanakin rayuwarsa.

Wakilin jami'ar Almustafa a yankin tsakiyar asia Mohsen Dadsarasht ya bayyana cewa, ayyukan ibada da suke cikin watan ramadan tsari ne ga dukkanin sauran kwanakin rayuwarsa, wanda idan ya bi su zai samu kamala a cikin rayuwarsa.

A cikin bayanin da yake gabatarwa wanda ake sakawa a cikin faifan bidiyo da ake watsawa a wasu kafofin yada labarai, malamin ya bayyana cewa, manufar tarbiyantar da ruhi da jikin dan adam a cikin watan bisa bautar Allah, ita ce domin jikin ya saba kuma ya ci gaba haka a sauran rayuwarsa.

Ya ce azumi na nafila da sauran ayyukan nafila da ake yi a watanni da ba na ramadan ba, suna a matsayin ci gaba ne na ayyukan da aka fara daga watan domin dan adam ya mayar da ibada cikin tsarin rayuwarsa ta yau da kullum ba sai cikin ramadan ba.

3963957

 

 

 

captcha