IQNA

Ramadan Dama Ce Ta Gina Kyakkyawar Zamantakewar Al'umma

18:09 - April 20, 2021
Lambar Labari: 3485829
Tehran (IQNA) Wakilin jami’ar Almustafa a Amurka da Canada ya bayyana cewa, Ramadan dama ce ta gina kyakkyawar zamantakewa.

A rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, wakilin jami’ar Almustafa a kasashen Amurka da Canada Sheikh Mohsen Radmard ya bayyana cewa, shi lokaci na Ramadan wata bababr dama ce ta gina kyakkyawar zamantakewar al’umma.

Malamin ya ci gaba da cewa, lokacin azumin watan lokaci ne wanda ya banbanta da sauran lokuta a cikin rayuwar al’ummar musulmi, kasantuwar cewa lokaci ne na ibadar azumi, wannan yana bayar da damar karfafa sauran bangarri na ayyukan ibda fiye da sauran lokutan shekara.

Ta fuskar zamantakewar al’umma, taimakon raunana marassa galihu da ciyar da mabukata, da sauran ayyukan alhairi, sun fi yawa a cikin watan Ramadan a tsakanin musulmi fiye da kowane lokacia  cikin sauran lokuta na shekara.

Ya ce wanann yanayin na watan Ramadan, jin kai da taimako da ciyarwa, ana bukatar ya ci gaba ne har zuwa sauran lokuta na shekara, wanda hakan ke nufin cewa abin da aka samu na wanann tarbiya ta zama jiki a tsakanin al’ummar musulmi.

رمضان فرصتی برای جامعه‌سازی است + فیلم

 

3963970

 

 

captcha