IQNA

Watan Ramadan Babbar Dama Ce Ta Kara Samun Kusanci Da Allah Madaukakin Sarki

23:52 - April 26, 2021
Lambar Labari: 3485847
Tehran (IQNA) Sayyid Hashem Musawi shugabancin cibiyar musulunci ta birnin Landan ya bayyana watan Ramadan a matsayin babbar dama ta kara samun kusanci da Allah.

A cikin bayanansa da yake gabatarwa da ake sakawa a shafukan yanar gizo dangane da watan Ramadan, Sayyid Hashem Musawi shugabancin cibiyar musulunci ta birnin Landan ya bayyana watan Ramadan a matsayin babbar dama ga musulmi ta kara samun kusanci da Allah maadaukakin sarki.

Inda ya ce musulmi yana samun dama ta tarbiyar ruhi a cikin watan ramadan fiye da kowane lokaci, domin kuwa azumi na kwanaki ashirin da tara ko talatin a jere, da kuma ayyukan ibada da yake yi da Allah ke ninka ladarsu, da falala mai yawa ta Allah madaukakin sarki da ke cikin wanann wata da masu bautar Allah suke samu, babbar riba ce ga musulmi.

Ya kamala bayaninsa da cewa, musulmi ya yi amfani da wannan damar domin samun kusanci da Allah madaukakin sarki.

3966000

 

captcha