A cikin wani jawabinsa da ya gabatar, Sayyid Hashem Musawi shugaban cibiyar musulunci ta birnin Landan na kasar Burtaniya ya bayyana cewa, natsuwar ruhi na daga cikin muhimman hanyoyin da ke taimaka wa mumuni wajen fahimtar ma'anonin kur'aani kur'ani mai tsarki.
Ya ce lokacin azumin watan yana daga cikin lokuta da musulmi yake samun natsuwar ruhi, saboda ladabtar da jikinsa da yake yi da kuma tarbiyantar da shi a kan bautar Allah fiye da kowane lokaci.
Ya kara da cewa,a duk lokacin da musulmi ya yi amfani da damar da ya samu a cikin wannan lokaci mai albarka wajen kara samun kusanci da Allah, to ruhinsa zai kara samun natsuwa, kuma kofofin fahimta za su kara bude masa, daga ciki kuwa da fahimtar ma'anoni na zancen Allah madaukakin sarki.