IQNA

Dalibin Jami'a Wanda Ya Kware Wajen Kwaikwayon Muryoyin Fitattun Makaranta Kur'ani Na Duniya

14:44 - April 28, 2021
Lambar Labari: 3485856
Tehran (IQNA) Abdulrahman Ashraf dalibin jami'a ne a kasar Masar wanda ya kware wajen kwaikwayon muryoyin manyan makarantan kur'ani na duniya.

Jaridar Yau Sabi ta bayar da rahoton cewa, Abdulrahman Ashraf dalibin jami'a ne wanda aka haife a garin Tanta na kasar Masar, wanda ya kware wajen kwaikwayon muryoyin manyan makarantan kur'ani na duniya.

Ya ce tun yana karami ya fara koyon hardar kur'ani, inda ya hardace juzu'i 21 wato izihi arba'in da hudu a wajen wani malami, daga bisani kuma ya tafi makarantar sakandare, inda yake gudanar da karatun kur'ani a wuraren gasa da kuma idan an yi rasuwa.

Daga cikin amnyan makarantan da yake kwaikwayon muryarsua  wajen tilawa akwai Muhammad Siddiq Alminshawi, Abul Ainain, sheikh Muhamamd Shuhat Anwar, Sheikh Abdulfattah Taruti, sheikh Hujjaj Alhindawi, da kuma limaman masallacin haramin Makka mai alfarma.

3966979

 

captcha