IQNA

Ranar Quds Ta Duniya Rana Ce Ta Nuna Dukkanin Goyon Baya Ga Al'ummar Falastinu

21:24 - May 07, 2021
Lambar Labari: 3485888
Tehran (IQNA) ranar Quds ta duniya ta nuna cikakken goyon baya ga al'ummar Falastinu da kuma fata kan 'yantar da masallacin Aqsa.

Shekaru arba’in  da suka gabata a rana irin ta yau Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma na shekara ta 1399, marigayi Imam Khomaini ya ayyna wannan ranar da ta zama ranar nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu da kuma kare masallacin Quds mai alfarma, inda ya bayyana wannan ranar a matsayin ranar Quds ta duniya, kuma ya yi ga dukkanin msuulmi das u raya wannan rana a ko’ina suke a duniya.

Tun daga wanan lokacin ne aka fara gudanar da tarukan ranar Quds ta duniya a kasar Iran da kuma gudanar da jerin gwano domin nuna goyon baya ga al’umar falastinu, da kuma yin tir da Allawadai da keta alfarmar masallacin Quds mai alfarma da yahudawa suke yi.

A halin yanzu ana gudanar da tarukan wanann rana ta Quds ta duniay a koina a cikin fadin duniya, da hakan ya hada hard a cikin kasshen turai, domin tabbatarwa duniya cewa musulmia duik inda suke suna tare ad ‘yan uwansu Falastinawa da ake zalunta, da kuma neman a kare hakkokinsu da yahudawa suka kwace musu a cikin kasarsu.

 

3969890

 

captcha