Shafin yada labarai na albayan ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Muhyiddin Hafizullah wanda ya kwashe fiye da shekaru 50 a kowace rana yana a cikin masallacin manzon Allah (SAW) a Madina, ya rasu yana da shekaru 107.
Wannan dattijo wanda dan asalin kasar Afghanistan ne, mahardacin kur'ani mai tsarki ne, mafi yawan lokutan rayuwarsa yana a cikin masallacin manzon Allah ne yana tilawar kur'ani mai tsarki.
Wannan ne yasa mutane suke kiransa da makwabcin masallacin manzo (SAW) wanda a kowane lokaci idan ya yi sallar asubah a cikin masallacin, ya kan zauna a kusa da kabarin manzon Allah (SAW) yana karatun kur'ani, haka zai ci gaba da zama a cikin masallacin ko a harabarsa, har zuwa bayan kammala sallar isha'i.
Wadanda suka san shi sun tabbatar da cewa fiye da shekaru 50 da suka gabata haka yake rayuwarsa, inda a jiya Allah ya yi masa rasuwa yana da shekaru 107 a duniya.