IQNA

Matakin Amurka Na Rufe Shafukan Kafofin Yada Labaran Iran Da Wasu Na Yankin

23:36 - June 23, 2021
Lambar Labari: 3486041
Tehran (IQNA) matakin gwamnatin Amurka ta dauka na rufe shafukan wasu kafofin yada labaran Iran da wasu na yankin na ci gaba da fuskantar martani.

Gwamnatin kasar Amurka ta toshe hanyoyin shiga na gwamman shafukan intanet na yada labaran kasar dama na wadansu kungiyoyi dake da alaka da kasar ta Iran.

Kafofin da Amurka ta toshe shafukan nasu sun hada da tashar talabijin ta Press-TV, dake watsa shirye shiryen da turancin Ingilishi, da kuma tashar talabijin ta Al-Alam dake watsa shirye shirye da larabci, da kuma tashar Al-Masirah, ta ‘yan kungiyar Ansarullah ta Yemen, da kuma tashar Falastine Today, da ke da alaka da kungiyoyin gwagwarmaya na Falasdinu.

A nasa bangaren shugaban bangaren watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo na kasar zuwa kasashen ketare ya mayar da martani dangane da matakin da gwamnatin ta dauka na rufe shafukan wasu tashohin kasar.

A zantawarsa da tashar alalam, Shugaban bangaren watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo na kasar zuwa kasashen ketare ya bayyana cewa, tun bayan samun nasarar Falastinawa a kan yahudawan sahyuniya  a yakin baya-bayan nan da Isra’ila ta kaddamar kan al’ummar Gaza, muka yi zaton cewa haka za ta faru.

Ya ce wannan mataki da Amurka ta dauka na rufe shafukan wasu daga cikin manyan tashohin talabijin na kasar Iran da ke watsa shirye-shiryensu zuwa kasashen ketare, ba zai taba hana ci gaba da bayyana gaskiya ga al’ummomin duniya ba.

Kamar yadda kuma ya bayyana cewa, tun fiye da shekara biyu da suka gabata sun riga sun shirya ma hakan, domin kuwa rufe wadannan shafuka bai tsayar da shirye-shiryen wadannan tashohi ba, a kan tauraron dan adam da kuma wasu shafukan na yanar gizo.

Sakon da ke fitowa da zarar an bude shafukan, mai dauke da tambarin ‘yan sandan tarayya da kuma na ma’aikatar kasuwanci ta Amurka, ya nuna cewa ‘’ gwamnatin Amurka ta kame wannan shafin, a wani bangare na aiwatar da doka, bisa umarnin ofishin masana'antu da tsaro na Amurka, da ofishin kula da binciken ababen da ake shigowa da su da kuma ofishin tarayya na bincike.

Ko a watan Oktoban shekara data gabata, ma’aikatar shari’a ta Amurka sanar da kwace kusan shafukan yanar gizo 100 wadanda ta ce suna da alaka da dakarun kare Juyin Juya Halin musulinci na Iran, wadanda ta ce suna yada farfagandar Iran a duniya.

 

 

3979565

 

 

captcha