IQNA

Taro Kan Harkokin Tattalin Arziki Bisa Tsarin Musulunci A Kasar Tanzania

20:12 - July 02, 2021
Lambar Labari: 3486068
Tehran (IQNA) za a gudanar da zaman taro kan harkokin tattalin arziki bisa tsari na addinin muslunci a kasar Tanzania.

Shafin yada labarai na jaridar Pak Observer ya bayar da rahoton cewa, a ranar 8 ga wannan ta na Yuli za a gudanar da zaman taro kan harkokin tattalin arziki bisa tsari na addinin muslunci a birnin Dar Salam fadar mulkin kasar Tanzania.

Taron zai samu halartar masana kan harkokin tattalin arziki musulmi daga sassa daban-daban na kasashen nahiyar Afirka, wadanda za su gabatar da mahangarsu kan hanyoyin ci gaba da kara bunkasa harkokin tattalin arziki.

Tsaarin da ake tafiyar da shi bisa mahanga ta addinin musulunci ta fuskacin tattalin arziki dai ya hada da hada-hadar kiudade ta hanyar bankunan musulunci, da kuma kamfanoni masu samar da kayayyki na halal.

Wadannan cibiyoyi da bankuna na musulunci suna gudanar da harkokinsu ne tare da kiyaye abubuwan da muslunci ya haramta, da kuma kiyaye ka'idojin da ya shata a cikin mu'amaloli.

 

 

3981436

 

 

 

captcha