IQNA

Martanin Kungiyoyin Falastinawa Kan Bude Ofishin Jakadancin UAE A Isra’ila

18:04 - July 14, 2021
Lambar Labari: 3486105
Tehran (IQNA) kungiyoyin gwagwarmaya da sauran bangarorin al'ummar Falastinawa sun yi Allawadai da bude ofishin jakadanci da UAE ta yi a Isra'ila.

Batun bude ofishin jakadanci da UAE ta yi a yau a Isra'ila, yana ci gaba da fuskantar kakkausan martani daga bangarori daban-daban na al’ummar falastinu, da kuma al’ummomin larabawa daga kasashe daban-daban, wadanda suke bayyana hakan a matsayin cin amanar Falastinawa da kuma al’ummar musulmi.

A cikin bayanin da ta fitar a  yau kan wannan batu, kungiyar Hamas ta mayar da kakkausan martani a kan gwamnatin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ta bayyana hakan a matsayin babban zunubi da kuma cin amanar al’umma.

Hamas ta ce, abu mafi muni dangane da wannan mataki na Hadaddiyar Daular Larabawa shi ne, hakan yana zuwa ne ‘yan kwanakin bayan kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a kan Falastinawa a yankin Zirin Gaza, tare da kashe mata da kananan yara, maimakon daukar matakin ladabtarwa a kan Isra’ila, sai aka dauki matakin kara kulla dankon alaka da kauna a tsakaninsu.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa, a yau ne aka gudanar da bikin bude bude ofishin jakadanci na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato UAE, a birnin Tel Aviv fadar mulkin gwamnatin yahudawan Sahyuniya.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin yahudawa, da suka hada da shugaban Isra’ila Ishaq Herzog, da kuma ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Yair Lapid, gami da wasu daga cikin manyan jami’an Isr’ila, da kuma jami’an gwamnatin hadaddiyar daular larabawa, da kuma wasu jami’an gwamnatocin larabawa masu alaka da Isra’ila.

 

3984177

 

captcha