IQNA

Hamas Ta Soki Tarayyar Afirka Kan Amincewa Da Isra’ila A Matsayin Mamba Mai Sanya Ido A Kungiyar

21:54 - July 24, 2021
Lambar Labari: 3486134
Tehran (IQNA) Kungiyar Hamas nuna takaici matuka dangane da amincewa da Isra’ila a matsayin mamba 'yar kallo a kungiyar AU.

Bangarori daban-daban na al’ummar Falastinu sun nuna takaici matuka dangane da amincewa da Isra’ila a matsayin mamba mai sanya ido a kungiar tarayyar Afirka.

A cikin bayanai da kungiyoyi daban-daban na Falastinawa suka fitar dangane da amincewa da Isra’ila a matsayin mamba ‘yar kallo a kungiyar tarayyar Afirka, sun bayyana wannan matakin da cewa yana tattare da hadari kuma abin ban takaici ne.

Bayanin Falastinawa ya bayyana cewa, kasashen Afirka da dama suna nuan jarunta wajen kin amincewa da duk wani matsin lamba a kansu dangane da matsayar ad suke dauka wajen nuna goyon bayan ga al’ummar falastinu, da kuma kin amincewa da zaluncin da gwamnatin yahudawan Isra’ila take yi a kan al’ummar Falastinu.

A kan haka Falastinawan suka bukaci kungiyar tarayyar Afirka da ta sake yin nazari kan sanya Isra’ila a mayayin mamba a cikin wannan kungiya, domin hakan yana a matsayin abin da zai kara karfafa gwiwar Isra’ila ne wajen ci gaba da aikawar da siyasar kisan kiyashi a kan al’ummar Falastinu, kuma hakan tamkar ba ta lasisi ne da ke halasta mata yin hakan.

Falastinawan sun bayyana cewa, kasashen Afirka sun dandana zalunci na bakin mulki mallaka da nuna musu wariya da fin karfi a cikin kasashensu, wanda kuma a kan haka al’ummar Afirka ta yi gwagwarmaya da sadaukarwa domin samun ‘yanci daga zalunci da danniya da mamaya ta ‘yan mulkin mallaka, inda wannan shi ne abin da Isra’ila take yi kan Falastinawa a halin yanzu.

3986071

 

 

captcha