IQNA

Shugaban Masar Ya Bukaci Malamai Su kare Muslucni Ta Hanyar Yanar Gizo

21:15 - August 03, 2021
Lambar Labari: 3486165
Tehran (IQNA) shugaban kasar Masar ya bukaci malaman addinin muslucni da su dauki matakan fuskantar yada kin jinin musunci da ake ta hanyar yanar gizo.

A lokacin da ya zanta da manyan malamai daga kasashen duniya a yammacin yau  Talata, shugaban kasar Masar Abdulfattah Al Sisi ya bayyana cewa, nauyi ne da ya rataya kan malamai su mayar da hankali kan nuna kin jinin muslucni da ake yi ta hanyar yanar gizo a duniya.

Al Sisi ya bayayna cewa, bisa la'akari ad canjin da aka samu a duniya, ya zama wajibia  akn musulmi musamman ma malamai su mayar da hankali matuka ga farmakin da ake kai wa muslunci ko ta ina, musamman a shafukan yanar gizo.

Ya ce da dama daga cikin masu akidar kin jinin musulunci suna yada akidojinsu ne ta hanyar shafukan sadarwa, kuma hakan ya kan yi tasiria a cikin zukatan mutanen da ba su san addinin muslunci, wanda kuam nauyi kan malamai su ma su bayyana hakikanin koyarwa ta zaman lafiya da tausayi da 'yan adamtaka irin ta addinin muslunci.

A jiya ne aka kammala zaman taro na malamai mambobi a  cibiyar fatawa ta Azhar wadda take da rassa a kasashen duniya daban-daban, inda malamai mambobi wannan cibiya da suke wakiltar Azhar suka taru domin tattauna hanyoyi karfafa fatawoyi an addinin muslunci.

 

3988110

 

 

captcha