IQNA

Wata Mata 'Yar Turkiya Na Kuka Saboda Kur'anin Mijinta Ya Kubuta A Wata Ambaliyar Ruwa

22:47 - August 22, 2021
Lambar Labari: 3486229
Tehran (IQNA) wata mata 'yar kasar Turkiya tana kuka saboda murna bayan da kur'anin mijinta ya kubuta daga bacewa bayan wata ambaliyar ruwa.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, mata 'yar kasar Turkiya tana kuka ne saboda murna bayan da kur'anin mijinta  ya kubuta daga bacewa bayan wata ambaliyar ruwa, wanda kuma kimanin shekaru 35 da suak gabata a ka baiwa mijin nata kyautar wannan kwafin kur'ani mai tsarki.

Moray Ardenz shi ne mijin wannan mata 'yar shekaru 76 da haihuwa, sannan kuma shi da iyalansa suna zaune ne Uzluchi, inda suka rasa mafi yawan kayayyakin gidansu sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a ranar 11 ga watan Agustan nan da muke a ciki a kasar Turkiya.

Duk da cewa kayansu sun bata sakamakon ambaliyar ruwan, amma matarsa ta yi farin ciki maras misiltuwa saboda kur'anin mijinta bai bata ba, wanda masu ceto ne suka samu kur'anin a cikin ruwa ba tare da komai ya same shi ba.

شوق بانوی ترکیه‌ای از سالم‌ماندن قرآن پس از سیل + فيلم

 

 
 
captcha