A daidai lokacin da kwanaki 13 ne suka rage a gudanar da tarukan zirarar arbaeen a kasar Iraki, miliyoyin mutane daga ko'ina a cikin kasar suna ci gaba da yin tattaki zuwa Karbala.
Wanann yana zuwa ne a daidai lokacin da a nasu bangaren mahukuntan kasar suke daukar dukkanin matakan da suka dace na kiwon lafiyar jama'a da kuma tsaro.
Muhimman hanyoyin da ake domin isa Karbala sun hada da Najaf - Haidariyya - Karbala, Hillah - Tuwairij - Karbala, Baghdad - Musayyib - Karbala, Ainu al-tamr - Karbala, Kufah - Tuwairij - Karbala.
A dukkanin wadannan hanyoyi mutane da suke a garuwa da kauyuka ne suke wa masu tattakin hidima da abinci da sauran abubuwan bukatar rayuwa.