IQNA

Manyan Kusoshi 113 Na Kwamitin Zartarwa A Jam'iyyar Nahda A Tunisia Sun Yi Murabus

23:44 - September 25, 2021
Lambar Labari: 3486351
Tehran (IQNA) manyan kusoshi 113 na kwamitin zartarwa na jam'iyyar nahda a Tunisia sun yi murabus.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, manyan kusoshi 113 na kwamitin zartarwa na jam'iyyar nahda a Tunisia sun yi murabus daga mukaminsu.

Manyan mambobin na jam'iyyar Nahda su 113 sun yi murabus ne sakamakon abubuwan da suka biyo baya, bayan da jam'iyyar ta samu damar lashe zabukan majalisa, inda akasarin kujerun majalisar dokokin kasar na jam'iyyar Nahda ne, amma ba su tabuka komai ga al'ummar kasar ba.

Sakamakon yadda jam'iyyar Nahda wadda take da shugaban majalisar dokoki da kuma Firayi minista kasar Tunisia ta kasa tabuka komai ga al'ummar kasar, shugaban kasar Qais Saeed ya dakatar da aikin majalisar, da kuma jingine yin aiki da kundin tsarin mulkin kasar.

bayan rusa majalisar ministoci da jingine aikin majalisar dokoki, Qais Saeed ya kawo sabbin canje-canje a cikin harkokin gudanarwa na kasar ta Tunisia. 

Tun kafin wannan lokaci wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar nahda sun fice daga jam'iyyar, bayan da shugaban kasar ya rusa majalisar ministoci tare da jingine aikin majalisar dokoki da kuma kundin tsarin mulki.

Yanzu dai manyan jiga-jigan jam'iyyar ta Nahda da suka balle, suna shirin kafa sabuwar jam'iyyar siyasa wadda za ta fito da sabbin tsare-tsare.

 

4000046

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kwamitin zartarwa
captcha