IQNA

Farfesa Chris Heuer: Gwagwarmayar Imam Hussain Sadaukarwa Ce Domin Dukkanin 'Yan Adam

21:25 - September 28, 2021
Lambar Labari: 3486362
Tehran (IQNA) Farfesa Chris Heuer masani dan kasar Burtaniya, ya bayyana gwagwarmayar Imam Hussain (AS) da cewa sadaukarwa ce domin dukkanin 'yan adam.

A zanatawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, Farfesa Chris Heuer masani dan kasar Burtaniya, ya bayyana gwagwarmayar Imam Hussain (AS) da cewa sadaukarwa ce domin dukkanin 'yan adam su rayu a cikin 'yanci, ba a karkashin zalunci da mulkin mulukiya da kama karya ba.

Ya ce abin da Imam Hussain ya yi, shi ne ya kara tabbatar da matsayinsa na cewa shi mutum ne na musamman, kuma jagora ne wanda ya damu da al'ummarsa, wanda ya damu makomar addininsa da akidarsa, domin kuwa kin mika wuya da ya yi, shi ne ya wanzar da fahimtarsa da akidarsa da koyarwarsa har zuwa yau.

Farfesa Chris Heuer ya ci gaba da cewa, a matsayinsa na mai bincike ya iya gano cewa, kasantuwar Hussain jikan Annabi Muhammad (SAW) ne wanda ya samu tarbiya irin ta kakansa, wannan babban lamari ne a wurin musulmi, saboda haka kisan gillar da sarakunan Bani Umayya suka yi masa, yana a matsayin rusa gidan sarautarsu ne baki daya, kuma abin da ya faru kenan.

Haka nan kuma ya bayyana sadaukarwar Imam Hussain da cewa, ta zama abin buga misali ga masu gwagwarmayar neman 'yanci daga azzalumai da 'yan mulkin mallaka a duniya, wadanda wasunsu sun rika bayar da misali da cewa sun darasi ne daga tarihin gwagwarmayar Imam Hussain, wajen neman rayuwa a cikin 'yanci na 'yan adamtaka.

captcha