IQNA

Babbar Cibiyar Fatawa Ta Masar Ta Kirayi Musulmi Da Su Raya Ranakun Murnar Maulidin Manzon Allah (SAW)

20:30 - October 11, 2021
Lambar Labari: 3486413
Tehran (IQNA) babbar cibiyar fatawa ta kasar Masar ta kirayi musulmi da su fito su raya ranakun murnar Maulidin manzon Allah (SAW).

Shafin yada labarai na Sadal Balad ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ta fitar a shafinta na facebook, babbar cibiyar fatawa ta kasar Masar wato Darul Ifta, ta kirayi musulmi da su fito su raya ranakun murnar Maulidin manzon Allah (SAW).

Bayanin cibiyar ya ce akwai dalilai da dama da suka tabbatar da ingancin Maulidin manzon Allah (SAW) a cikin addinin muslunci, daga ciki kuwa har da cewa a lokacin manzon Allah yana raya wasu daga cikin sahabbai sun rika raya wannan rana tare da yin abubuwa na farin ciki, amma kuma bai hana su ba.

Baya ga haka kuma cibiyar ta kawo hadisin da ya zo a cikin littafai da dama, daga cikin har da littafin sahih Muslim, wanda ya kawo hadisi da aka karbo daga Abu Qatadah, cewa manzon Allah (SAW) ya ce yana yin azumin ranar Litinin ne domin murnanr cewa a wannan ranar ce aka haife shi, wato yana murna da kuma raya ranar da aka haife shi.

Cibiyar fatawar ta ce, manzon (SAW) yana yin yin murna da raya ranar da aka haife shi ne duk mako, saboda haka idan musulmi sun yi haka sau daya a shekara shi ne mafi karanci.

A kan haka cibiyar ta ce raya wannan rana ta Maulidin manzon Allah da karatun kur'ani, da addu'oi da zikirin Allah, da karatun baitocin wakokin yabon ma'aiki abu ne mai kyau, kuma manyan malamai a tarihin musulunci sun yi hakan, daga cikinsu akwai Ibn Jauzi, Ibn Kathir, Ibn Dahiyyah Al-andalusi, Ibn Hajar Asqalani, Jalaluddin Al-Suyudi da makamantansu, wadanda sun yi maulidin manzon Allah (SAW) kuma sun umarci musulmi da su yi domin samun lada da kuma albarkacinsa (SAW).

 

4003961

 

captcha