IQNA

Najeriya: ‘Yan Ta’adda Sun Saki Akalla Dalibai Da Malamai 90 Da Suka Sace A Jihar Kebbi

14:32 - October 13, 2021
Lambar Labari: 3486420
Tehran (IQNA) Hukumomin Najeriya sun ce an saki mutane 90, ciki har da dalibai da malamai da ‘yan bindiga suka sace ranar 17 ga watan Yuni a Kebbi.

Hukumomin Najeriya sun ce an saki mutane 90, ciki har da dalibai da malamai da ‘yan bindiga suka sace ranar 17 ga watan Yuni a Kebbi.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoto cewa, Hukumomin Najeriya sun sanar a ranar jiya  Talata cewa, an saki akalla dalibai da malamai 90 da wasu ‘yan bindiga suka sace a ranar 17 ga watan Yuni a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

A wannan ranar, wasu 'yan bindiga sun kai hari a makarantar sakandaren' yan mata ta tarayya da ke gundumar Birnin Yauri a jihar Kebbi, inda suka sace dalibai da malamai fiye da 90, sannan suka kashe jami'an 'yan sanda biyu da malamai hudu.

Majiyoyin tsaron Najeriya ba su bayar da cikakken bayani kan yadda aka sako wadanda aka sace ba, amma sun jaddada cewa gwamnatin Najeriya ta mika ‘yan matan dalibai da malaman ga iyalansu.

Gungun masu dauke da makamai a Najeriya kan kai hari kan makarantu don neman kudin fansa tare da yin garkuwa da dalibai da dama.

A watannin baya -bayan nan an kai hari kan makarantu da jami’o’i da dama a arewacin Najeriya tare da sace dalibai sama da 700 tun daga watan Disambar bara ya zuwa yanzu.

 

 

4004596

 

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya tarayya makarantar sakandare
captcha