IQNA

A Yau Talata An Bude Babban Taron Makon Hadin Kan Musulmi Na Duniya A Kasar Iran

18:37 - October 19, 2021
Lambar Labari: 3486446
Tehran (IQNA) an bude taron makon hadin kan musulmi karo na 35 da aka saba gudanarwa a kowace shekara a kasar Iran.

A yau ne aka bude taron makon hadin kan musulmi karo na 35 da aka saba gudanarwa a kowace shekara a kasar Iran.

A wannan karon an baiwa taron taken hadin kan Musulmai domin zaman lafiya da nisantar rikici da fada tsakanin kasashen Musulmi.

Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ne ya fara bude taron da bayani ga mahalarta taron, inda ya bayyana cewa wannan taron yana da muhimmnci matuka  wajen fadakar da alumma musulmi su fahimci hakikanin makircin da makiya suke kulla musu.

Ya ce, a yau muna kallon yadda makiya suke kulla makirci da haifar da rarraba tsakanin kasashen musulmai musaman a wannan yanki namu, inda kasasshen Iraki, Siriya , Afghanistan, Labanon da Yamen suke a matsayin babban misali kan hakan.

A kan haka ya ce, ya zama wajibi mu hada karfi da karfe waje guda domin kare hadin kai dake tsakaninmu da tunkarar makircin da makiya musulunci da musulmi suke kullawa al’ummar musulmi domin raunana ta.

Taron na makon hadin kai karo na 35 da aka fara a yau Talata zai ci gaba da gudana har zuwa ranar 24 ga watan na Oktoba da muke ciki, wanda kuma a ranar ne za a kawo karshensa.

Marigayi Imam Khomeini ne dai ya assasa wannan taro na makon hadin kan al’ummar msuulmi, wanda ya sanya makon haihuwar manzon Allah ya zama shi ne makon hadin kan musulmi.

 

4006238

 

 

 

captcha