IQNA

Sallar Rokon Ruwa A Masallacin Haramin Makka Da Masallacin Manzon Allah (SAW) A Madina

19:28 - November 04, 2021
Lambar Labari: 3486513
Tehran (IQNA) an gudanar da sallar rokon ruwa a masallacin haramin Makka da kuma masallacin manzon Allah (SAW)

A rahoton da shafin yada labarai na Al-Balad ya bayar, a yau Alhamis masu ibada a Masallacin Harami da Masjidul Nabi sun gudanar da sallar rokon ruwan sama.
 
Sallar ta biyo bayan kiran da Sarkin Saudiyya ya yi ne ga dukkanin al'ummar kasar Saudiyya, na su gudanar da sallar rokon ruwa saboda matsalar karancin ruwan sama da ake samu a  kasar.
 
Ofishin masarautar Saudiyya a cikin wata sanarwa da ya fitar kwanaki biyu da suka gabata ya ce: A bisa sunnar Manzon Allah (S.A.W) idan an samu matsalar karancin ruwan sama, ana fita zuwa sallar rokon ruwa.
A akn haka sarkin ya jaddada muhimmancin gudanar da wannan salla a fadin kasar domin rokon Allah da ya saukar musu da ruwan sama.
 
 

4010669

 
captcha