IQNA

Paparoma Ya Yi Tir Da Yunkurin Kisan Firayi Ministan Iraki

19:10 - November 09, 2021
Lambar Labari: 3486534
Tehran (IQNA) Paparoma Francis ya yi tir da yunkurin kisan firayi ministan Iraki wanda bai yi nasara ba.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a cikin sakon da fadar Vatican ta aike wa  firayi ministan Iraki Mustafa Alkazimi da sunan Paparoma Francis, ta yi tir da yunkurin kisan firayi ministan na Iraki wanda bai yi nasara ba.

Fadar Vatican ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar ta aike da sakon nuna goyon baya ga firaministan Iraki da Paparoma Francis ya sanya wa hannu.
 
A cikin wasikar ta yi Allah wadai da wannan danyen aikin ta'addanci, Paparoma ya jaddada fatansa na cewa, da yardar Allah al'ummar Iraki za su ci gaba da bin tafarkin zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da hadin kan 'yan uwantaka da kwanciyar hankali."
 
Idan dai ba a manta ba Paparoma Francis shugaban mabiya darikar Katolika na duniya ya je kasar Iraki a wata ziyarar tarihi a cikin watan Maris din da ya gabata, inda ya gana da Ayatullah Sistani da wasu jami'an addini da na siyasa na wannan kasa.
 
Jami’an tsaro da na sojan Iraqi sun ce jiragen yaki marassa matuki guda uku ne suka kai farmaki kan gidan al-Kazhimi a daren Lahadin da ta gabata, inda suka lalata biyu daga cikinsu, na uku kuma ya kai hari kan gidan Firayim Minista.
 
Yunkurin kisan gillar da aka shirya yi wa Mustafa al-Kazemi ya gamu da martani da tofin Allah tsine daga kasashe da dama, yayin da kuma wasu ke ganin cewa an tsara shirin ne daga wajen kasar Iraki, da nufin sake kasar cikin wani hali, bayan da ta fara farfadowa daga halin da aka jefa ta a ciki a baya, ta hanayar haifar da ayyukan ta'addancia  cikin kasar.

 

4011992

 

 

 

 
 

 

captcha