Hukumomi a jihar Maradi dake kudancin Jamhuriyar Nijar, sun ayyana zaman makoki na kwanaki uku, biyo bayan iftila’in gobara data auku a wata makarantar renon yara da ta yi ajalin yara 25.
Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta sanar yayin taron majalisar ministocinta ta ce yara 25 ne suka rasu a gobarar, kana wasu 14 suka jikkata ciki har da biyar dake cikin mawuyacin hali.
Tuni gwamnatin kasar ta haramta amfani da azuzuwa zana a cikin kananan makarantu a duk fadin kasar.
Ko a watan Afrilu da ya gabata sama da yara ashirin ne suka rasa rayukansu a irin wannan gobara a wata makarantar yara a Yamai babban birnin kasar.
A wani labarin kuma mutum fiye da talatin ne suka rasa rayukansu biyo bayan ruftawar wata mahakar zinari ta gargajiya a garin Dan Isa dake jihar Maradi.