IQNA

Haniyya: Batun Fursunoni Falastinawa Ne Ya Fi Damun Kungiyar Hamas

16:06 - November 11, 2021
Lambar Labari: 3486540
Tehran (IQNA) Hamas ta ce batun fursunonin Falastinawa da Isra’ila ke tsare da su shi ne mafi muhimmanci a wurinta.
Shugaban kungiyar gwagwarmayar Falastnawa ta Hamas Isma’il Haniya ya bayyana cewa, batun fursunonin Falastinawa da Isra’ila ke tsare da su shi ne mafi muhimmanci a wurinsu.
 
A wata tattaunawa ta wayar tarho da wasu fursunonin guda biyu, Qassami Muhammad Jaber Abdu da Majdi al-Qubisi daga Ramallah, wadanda aka sako su bayan shekaru da dama da Isra’ila ta yi garkuwa da su, Ismail Haniyeh ya jaddada mahimmancin batun fursunonin Falastinawa da ke hannun gwamnatin yahudawa.
 
Haniyeh ya yaba da tsayin daka da wadannan fursunoni biyu suka yi a gidajen yarin gwamnatin sahyoniyawa, ya kuma yaba da kyakkyawar tarbar da dubban Falastinawa suka yi musu a yammacin gabar kogin Jordan.
 
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, yanayin da fursunonin Falasdinu suke ciki a gidajen yarin Isra'ila ba ya da kyau, kuma ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Ramallah ta sanar da cewa wasu fursunonin Falasdinawa hudu sun mutu sakamakon irin mawuyacin halin da suke ciki.
 
Wasu fursunoni 6 na Falasdinawa na ci gaba da yajin cin abinci a gidajen yarin Isra'ila domin nuna adawa da tsare su na wucin gadi, kuma lafiyar fursunonin shida na kara tabarbarewa a kowace rana, kuma cibiyoyin shari'a sun sha yin gargadi kan yiwuwar su rasa rayukansu.
captcha