IQNA

Gwamnatin Falastinawa Ta Soki Burtaniya Kan Saka Hamas A Cikin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda

16:54 - November 20, 2021
Lambar Labari: 3486583
Tehran (IQNA) Gwamnatin kwarya-kwaryan cin gashin kai ta Falastinawa ta yi kakkausar suka kan saka kungiyar Hamas a cikin kungiyoyin 'yan ta'adda da gwamnatin Burtaniya ta yi.

Gwamnatin kwarya-kwaryan cin gashin kai ta Falastinawa ta yi kakkausar suka kan matakin na gwamnatin Burtaniya, tare da bayyana hakan a matsayin halasta abin da Isra’ila ke yi na kisan kiyashi da cin zarafin al’ummar Falastinu.
 
Bayanin ya ce har kullum Burtaniya matsayinta dangane da takaddamar da ke tsakanin falastinawa da kuma yahudawa 'yan mamaya da suka mamaye mjsu kasa, shi ne daukar matsaya ta nuna goyon baya ido rufe ga dukkanin ta'asar da yahudawa suke tafkawa kan a'ummar falastinu.
 
Baya ga matsayin gwamnatin falastinawa, su ma a nasu bangaren kungiyoyin Falastinawa suna ci gaba da yin tir da Allawadai da wannan mataki na gwamnatin Burtaniya, tare da jaddada goyon bayansu ga Hamas, da kuma dukkanin kungiyoyi masu gwagwarmaya domin kubutar da Falastinu daga mamayar yahudawan sahyoniya.
 
Sakatariyar harkokin wajen kasar ta Burtaniya tana shirin mika wannan daftarin kudiri ga majalisar dokokin kasar domin kada kuri’ar amincewa ko rashin amincewa da shi, wanda kuma ake sa ran majalisar za ta amince saboda 'yan jam'iyyar consevative masu mulki kuma masu tsattsauran ra'ayi wadanda kuma su ne masu rinjaye a majalisar.
 
 

4014609

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Burtaniya
captcha