IQNA

Duk Da Matakan Da Isra'ila Ta Dauka Dubun-Dubatar Falastinawa Sun Yi Sallar Juma'a A Cikin Masallacin Quds

18:05 - November 26, 2021
Lambar Labari: 3486608
Tehran (IQNA) duk da irin matakan da Isra'ila ta dauka a yau amma dubban Falastinawa sun yi sallar Juma'a a cikin masallacin Quds mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran Safa ya bayar da rahoton cewa, dubun dubatar musulmi masu ibada ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa a daidai lokacin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta tilasta wa masu ibada shiga masallacin ta kofar tsohon birnin da kuma takura su.

Dakarun mamaya sun kafa shingaye a kofar shiga tsohon birnin da ke kan hanyar zuwa Masallacin Al-Aqsa, inda suka yi wa matasan tambayoyi tare da duba kowannen su, tare da duba kayansu da jakunkuna.
 
Masu ibada a masallacin Al-Aqsa sun gudanar da addu'o'i ga ruhin shahidai. An sanya manya-manyan tutoci a farfajiyar masallacin, a jikinsu akwai hotunan shahidai guda biyu Fadi Abu Shekhidam da Al-Fati Omar Abu Asb.
 
'Yan sandan gwamnatin mamaya sun kai farmaki a masallacin Al-Aqsa bayan sallar Juma'a tare da kwashe hotunan shahidan biyu.
 
Ofishin bayar da agajin gaggawa na Musulunci ya sanar da cewa, masallata 40,000 ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa a yau.
 
https://iqna.ir/fa/news/4016376

 

captcha