Sashen adana rubuce-rubuce da takardu masu alaka da hubbaren Alawi ya sanar da cewa, ana dawo da wani tsohon kur'ani mai tsarki da aka rubuta tun karni na 12 bayan hijira a cibiyar.
Hussein al-Sheibani, shugaban sashen, ya ce game da kokarin da aka yi na maido da wannan tsohuwar taswirar kur'ani: ya zama wajibi a gudanar da aikin sake gyara takardunsa.
Ya kara da cewa: "Wannan sigar ta riga ta wuce matakai da yawa ya zuwa yanzu, kuma ana cikin mataki kusan na karshe wajen aikin, wanda zaran an kammala za a fitar das u zuwa wuraren ajiye kayan tarihi na hubbaren.