IQNA

Alhuthi: Matsin Lamba Kan Al’ummar Yemen Ba Zai Sanya Su Mika Wuya Ba

20:34 - December 02, 2021
Lambar Labari: 3486635
Tehran (IQNA) Jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Alhuthi ya jaddada cewa, matsin lamba da hare-hare ba za su taba sanya al’ummar Yemen su mika wuya ba.

Tashar Almasirah ta bayar da rahoton cewa, Jagoran Ansarullah na kasar Yemen ya ci gaba da cewa: Al'ummar kasar Yemen na ci gaba da gudanar da rayuwarsu, duk kuwa da irin wahalhalu da matsaloli da takunkumi da kuma mawuyacin yanayi na tattalin arziki.

Sayyid Abdul Malik al-Houthi ya jaddada cewa makiyan kasar Yemen sun yi kokarin kawar da rayuwa a kasar ta hanyar kisan kai, da saka mutane cikin yunwa, takunkumi da yaki mai tsanani domin tilasta al’ummar kasar mika wuya ga manufofi na mulkin mallaka.

Jagoran Ansarullah ya ce "A yau muna aike da sako ga makiya ta hanayar yin tsayin daka tare da tinkarar dukkanin matsalolin da suka haddasa ma al’ummar kasar Yemen."

A wata ganawa da ya yi da tawaga daga lardin al-bayda a cikin wannan mako, Sayyid Abdul Malik ya kuma dora alhakin irin barnar da aka yi wa al'ummar lardin Al-bayda a kan masarautar Saudiyya wadda take kaddamar da yaki a kan al’ummar kasar.

Ya kara da cewa tarurrukan da suke gudana tsakanin al'ummar kasar Yemen na nuni da hakikanin 'yan uwantaka, hadin kai da amincewar da ke tsakaninsu.

Al-Houthi ya ce; ci gaba da yin tsayin daka da kin mika wuya ga manufofin makiya masu son yin mulkin mallaka a kan kasar Yemen, shi kadai mafita, kuma da taimakon Allah wadanda ake zalunta ne dai daga karshe suke samun taimakon ubangiji a kan azzalumai.

4017985

 

captcha