IQNA

An Kutsa Cikin Wayoyin Wasu Jami'an Amurka Da Manhajar NSO Ta Isra'ila

14:48 - December 04, 2021
Lambar Labari: 3486640
Tehran (IQNA) Reuters ya bayar da rahoton cewa kutsa cikin wayoyin wasu jami'an Amurka ta hanyar yin amfani da manhajar kamfanin NSO na isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, an yi amfani da manhajar kamfanin NSO na isra’ila wajen yin kutse a cikin wayoyin hannu na wasu jami’an gwamnatin Amurka.

Rahoton na kamfanin dillancin labaran reuters ya ce, an yi amfani da manhajar ne wajen kutsawa a cikin wayoyin jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka, tare da yin leken asiri a cikin bayanan  da wayoyin nasu suke dauke da su.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, bayanan da aka yi kutse a cikinsu sun shafi kasar Uganda ne, duk kuwa da cewa rahoton ya ce ba a iya gane takamaimai wanda ya yi amfani da manhajar wajen yin wannan aikin leken asiri ba.

Sai dai a nasa bangaren kamfanin na NSO na Isra’ila ya sanar da cewa, ba shi da masaniya kan a bin da ya faru, amma zai gudanar da kwakkwaran bincike kan lamarin, sannan kuma idan aka gano jami’in leken asirin da ya yi amfani da manhajar ta NSO, to za a dakatar da yin aiki tare da shi, sannan kuma za a dauki matakai na shari’a a kansa.

Sai dai a nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka taki ta ce uffan a kan wannan batu, duk kuwa da cewa wannan ba shi ne karon farko da ake bankado ayyukan leken asirin da Isra’ila ke yi kan jami’an gwamnatin Amurka ba.

 

 

4018251

 

captcha