IQNA

Azhar Ta Yi Gargadi Dangane Da Sabbin Dabarun ISIS Na Kai Hare-Haren Ta'addanci

19:28 - December 08, 2021
Lambar Labari: 3486658
Tehran (IQNA) Al-Azhar ta yi gargadi kan sabbin dabarun kungiyoyin 'yan ta'adda, musamman ISIS, na kai hare-haren ta'addanci.

Shafin Alwafd ya bayar da rahoton cewa, Al-Azhar ta yi gargadin cewa kungiyoyin 'yan ta'adda, musamman ISIS, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen yin amfani da na'urorin fasaha da fasahar zamani wajen aiwatar da makircinsu na ta'addanci da kutsawa yankuna daban-daban, musamman a nahiyar Turai.

Cibiyar da ke sa ido kan lamurran musulmi da ke karkashin Azhar ta bayar da rahoton cewa, wadannan kungiyoyi sun koma amfani da sabbin kayan aiki don kai hare-haren ta'addanci saboda wasu matsaloli da suke fuskanta,  da suka hada da asarar da dama daga cikin mayakansu.
 
Cibiyar ta ce "Binciken da muka gudanar ya nuna cewa kungiyoyin 'yan ta'adda, musamman ISIS, suna da sha'awar kai hare-hare ba tare da bata lokaci ba ta hanyoyi masu sauki da kayan aiki masu sauki, kamar sace mutane a wuraren masu cunkoson jama'a, ko kuma yin amfani da da makamai da za su iyin kisa cikin sauki.
 
 

 

4019294

 

captcha