Kamfanin dillancin labaran kasar Iraki ya habarta cewa, tawagar ta bayyana cewa: "Muna matukar yin Allah wadai da harin bam na ta'addanci a birnin Basra, muna mika ta'aziyyarmu ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya da kuma samun sauki cikin gaggawa." .
Ta ci gaba da cewa hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika, da kuma karfafa hadin kan kasa shi ne zai kawo cikas ga wannan yunkuri na neman kawo rudani a Iraki.
Da alama kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban da suka koma suna gudanar da ayyukansu a asirce bayan fatattakarsu da dakarun Iraki suka yi a baya-bayan nan sun fara fadada ayyukansu tare da shirya hare-hare da dama a nan gaba.
Halin da ake ciki na rashin tabbas ta fuskar siyasa a kasar Iraki, kasancewar sojojin mamaya na Amurka na ci gaba da wanzuwa a kasar, da kuma tasirin nasarorin da aka samu a kan 'yan ta'adda a kasar Siriya, da kuma shigo da wasu daga cikin 'yan ta'adda da suka tarwatse a Syria zuwa kasar Iraki, na daga cikin abubuwan da suke yi tasiri wajen sake dawowar irin wadannan ayyuka na ta'addanci a kasar.