IQNA

Tsohon Ministan Yada Labaran Lebanon Da Aka Tilasta Wa Murabus Ya Godewa Kungiyar Hizbullah

16:23 - December 09, 2021
Lambar Labari: 3486662
Tehran (IQNA) tsohon ministan yada labaran kasar Lebanon da aka tilasta wa yin murabus ya jinjina wa kungiyar Hizbullah.

Tsohon ministan yada labarai na kasar Labanon George Qardahi ya bayyana cewa: Hizbullah tana ganin cewa matsayina kan batun yakin Yemen na ‘yan adamtaka ne, a kan haka kungiyar ta goyi bayana, Don haka ina godiya ga Hizbullah.
 
Tsohon ministan yada labaran kasar Labanon George Qardahi ya bayyana a sabon martanin da ya mayar dangane da murabus din nasa: "Shawarar murabus da na yi, na yi hakan ne don kashin kai na kuma ba na neman mukami".
 
“A dangane da haka, Hizbullah tana ganin cewa matsayina na ‘yan adamtaka ne don haka ta goyi bayana, kuma ina yaba wa Hizbullah, kuma ina fatan dukkanin bangarorin siyasar kasar Lebanon matsayinsu ya zama mai cin gashin kansa, maimakon zama ‘yan amshin shata saboda abin duniya".
 
Tsohon ministan yada labaran na Labanon ya jaddada cewa, na shaida wa "Bishara Peter al-Rai'i" Bishop na Kiristan Maroni na Lebanon cewa zan yi murabus idan har akwai tabbacin murabus dina zai yi tasiri mai kyau kan alakar Saudiyya da Lebanon, kuma Al-ra’i ya tambayi jakadan Saudiyya kan hakan, amma kuma har yanzu bai bayar da amsa ba.
 
A hukumance Qardahi ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya kara jaddada matsayarsa na kiran Saudiyya da ta kawo karshen yakin da take kaddamarwa kan al’ummar kasar Lebanon, tare da sheda cewa yakin ba shi da wani amfani ga kowa hatta ga ita kanta gwamnatin Saudiyya.
 
Qardahi ya fuskanci matsin lamba daga masarautar saudiyya ne sakamakon furucin da ya yi tun kafin ya zama ministan Lebanon, inda ya kirayi Saudiyya ta da ta daina yakin da take yi kan al’ummar yemen, tare da bayyana yakin da cewa wauta ce.
 
A kan Saudiyya ta matsa ma gwamnati Lebanon lamba a kan dole ya yi murabus, tare da dorawa Lebanon takunkumai na siyasa, da kuma tilasta wasu kasashen larabawa ‘yan amshin shata daukar irin wannan matakin a kan Lebanon.
 
Bayan murabus din ministan yada labaran kasar Labanon George Qardahi bisa matsin lamba na ciki da waje, Sheikh Naeem Qasim mataimakin babban magatakardar na Lebanon ya bayyana a wata hira da aka yi da shi ta talabijin cewa, ya kamata Saudiyya ta kalli Lebanon a matsayin kasa mai cin gashin kanta, ba kasar da ke karkashin mulkin mallaka ba.
 
https://iqna.ir/fa/news/4019618
captcha