IQNA

Gwamnati Iraki Ta Ce An Kawo Karshen Yakin Da Kawance Amurka Ke Jagoranta A kasar

20:55 - December 09, 2021
Lambar Labari: 3486664
Tehran (IQNA) shugaban majalisar tsaron kasa a Iraki ya sanar da cewa, an kawo karshen yakin da sojojin kawancen Amurka suke yi a Iraki.
Kassim al-Araji, shugaban majalisar tsaron kasa a Iraki  ya sanar a hukumance cewa an kawo karshen yakin da dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta a Iraki da yammacin yau.
 
Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa a yau Alhamis, a zagaye na karshe na tattaunawa da jami'an kawancen kasashen duniya da aka fara a bara, a hukumance mun sanar da kawo karshen aikin soji da kuma ficewarsu daga Iraki.
 
Ya kara da cewa: Daga yanzu za a ci gaba da hulda da dakarun hadin gwiwa a fagen ba da shawarwari, horarwa da karfafa gwiwa.
 
A ranar 5 ga Janairu, 2020, kwanaki biyu bayan kisan Qassem Soleimani da al-Mohandes, majalisar dokokin Iraki, ta amince da korar sojojin Amurka tare da ayyana ta a matsayin doka.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4019727
captcha