IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Duniya A Kasar Masar

15:44 - December 11, 2021
Lambar Labari: 3486669
Tehran (IQNA) An fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 28 a kasar Masar da halartar dimbin malaman kur'ani daga kasashe daban-daban da kuma jawabin Mufti na Masar da Sheikh Al-Azhar.

A yau ne aka gudanar da bikin bude gasar kur’ani mai tsarki ta duniya karo na 28 a kasar Masar, kamar yadda shafin jaridar Al-Yawm Al-Sabeeh ya bayyana.

An shirya gasar ne karkashin kulawar shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi, an sanya wa gasar sunan Sheikh Mohammed Siddiq al-Manshawi, kuma an fara ta ne da karatun kur'ani mai tsarki wanda daya daga cikin wadanda suka yi nasara a shekarun baya ya gabatar.

A wajen bikin, babban Mufti na kasar Masar, Dakta Shoghi Alam, ya bayyana cewa, muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki a gasar kur'ani mai tsarki ta duniya: "Ba mu taru ba face sai saboda littafin Allah." Wannan babbar al'umma ce da ke rook da kur’ani a matsayin hanyar isa zuwa  ga Allah.

Akwai mahalarta gasar kur’ani mai tsarki ta duniya 74, da alkalai 12 daga ciki da wajen kasar Masar, kuma za a ba da kyautar fam dubu dari na Masar, kwatankwacin dalar Amurka 6,500 a matsayin wata kyauta ta karfafa gwiwa ga wadanda suka nuna kwazo a gasar a kowane fanni.

 

آغاز مسابقات بین‌المللی قرآن مصر + عکس

آغاز مسابقات بین‌المللی قرآن مصر + عکس

آغاز مسابقات بین‌المللی قرآن مصر + عکس

آغاز مسابقات بین‌المللی قرآن مصر + عکس

آغاز مسابقات بین‌المللی قرآن مصر + عکس

آغاز مسابقات بین‌المللی قرآن مصر + عکس

https://iqna.ir/fa/news/4020127

captcha