IQNA

An Dakatar Da Nuna Fim kan Falastinu Da Ya Jawo cece-Kuce A Jordan

21:51 - December 11, 2021
Lambar Labari: 3486671
Tehran (IQNA) Daraktan kamfanin "Amira" na kasar Masar "Mohammad Ziab" a hukumance ya sanar da dakatar da nuna fim din a kasar Jordan bayan zanga-zangar da aka yi a kasar.

Mohammad Ziab ya yi kira da a kafa kwamitin da ya kunshi fursunoni da iyalansu don kallo da kuma bayyana ra’ayinsu kan fim din.

Kamfanin Amira (Princess) shi ne wakilin Jordan a cikin kyautar  Oscar, wanda aka shirya fim di tare da haɗin gwiwar Masar, UAE, Jordan da Saudi Arabia, wanda aka samar a cikin 2021.

Ofishin Yada Labarai na cibiyar kula Fursunoni na Falasdinawa ya kuma yi kira da a kaurace wa fim din da Jordan ta zaba don kyautar Oscar wanda kuma shi ne fim Mafi kyawu a wurin kyautar wanda ba na Turanci ba.

Ofishin cibiyar da ke Gaza ya fitar da wata sanarwa inda ya bukaci al'ummar Palastinu da kuma kasashen Larabawa da su dage wajen kaurace wa fim din tare da tilasta wa masu shirya fina-finan su nemi gafara.

Sanarwar ta kuma yi kira ga kasar Jordan da ta janye bukatarta na bayar da lambar yabo ta Academy Awards na fim din.

Falastinawa dai suna ganin an ci zarafinsu ne a  cikin fim, inda maimakon a nuna irin zaluncin ad suke fuskanta daga Isra’ila, sai aka mayar da su tamkar su ne masu laifi.

4019904

 

captcha