IQNA

Isra'ila Ta Kame Falastinawa Fiye Da 400 A Cikin Watan Da Ya Gabata

20:45 - December 12, 2021
Lambar Labari: 3486674
Tehran (IQNA) Majiyoyin Falasdinawa sun ce gwamnatin sahyoniyawan ta kame Falasdinawa sama da 400 a watan da ya gabata.

Tashar Al-hurra ta bayar da rahoton cewa, Hukumomin Falastinu da ke bin kadun batun tsare fursunonin Falasdinawa a gidajen yari na Isra'ila sun bayyana cewa, mahukuntan gwamnatin mamaya sun kame Falasdinawa 402 a watan Nuwamban da ya gabata, da suka hada da mata da kananan yara.

Wata sanarwar hadin gwiwa da kwamitin kula da harkokin fursunoni Falastinawa (wanda ke da alaka da kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta PLO) da kungiyar fursunoni ta Falasdinu da gidauniyar kula da shahidai  da cibiyar yada labarai ta Wadi Al-Halwa ta ce: Isra'ila ta kame Falastinawan ne sama da 400 a cikin wata guda.
 
A cewar sanarwar, yawancin fursunonin sun fito ne daga birnin Kudus, kuma mutane 160 da suka hada da yara 54 na cikin su.
 
Hukumomin Falasdinu sun tattara bayanan cewa Isra'ila ta bayar da umarnin tsare mutane 123, gami da sabbin kararraki 39, a watan Nuwamban da ya gabata a sauran yankunan yammacin kogin Jordan.
 
Hukumar kula da fursunonin Falasdinu ta ce adadin fursunonin Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila ya kai 4,550, wadanda suka hada da fursunoni mata 32, da kananan yara 170 da ma'aikatan gudanarwa kusan 500.
 
 
 
 
 
 
 
 

 

captcha